BBC navigation

Hukuncin da aka yi wa John Terry shirme ne, in ji Barton

An sabunta: 28 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:32 GMT

Joey Barton

Dan wasan tsakiya na Queens Park Rangers Joey Barton ya bayyana matakin da hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dauka na dakatar da John Terry da cewa shirme ne kawai.

Hukumar ta dakatar da John Terry ne daga buga wasanni hudu, sannan ta ci tararsa fam 220,000 bayan ta same shi da laifin yin kalaman wariyar launin fata ga dan wasan QPR, Anton Ferdinand.

Barton ya ce ya kamata hukumar FA ta ji "kunyar" matakin da ta dauka.

Ya yi ikirarin cewa akwai gagarumin bambanci tsakanin dakatarwar da aka yi masa - ta watanni goma sha biyu- daga buga wasanni sakamakon rashin da'a da kuma hukuncin da aka yi wa Terry, wanda idan aka kwatanta nasa ya yi tsanani.

Barton ya rubuta a shafinsa na twitter cewa: ''Dakatarwar da aka yi wa Terry shirme ne ''.

Barton yana cikin 'yan wasan da suka buga gasar Premier League a watan Oktoba lokacin da Terry ya yi kalaman batanci ga Ferdinand.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.