BBC navigation

An fidda mutum-mutumin karon da zidane ya yi wa Materrazi

An sabunta: 28 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 18:54 GMT
zidane_ statue

Mutum-mutumin Zidane da Materrazi


A Paris an yaye mutun mutumin tsohon kyaftin din Faransa Zinedine Zidane lokacin da ya ke yiwa danwasan Italiya Materrazi karo a lokacin wasan karshe na gasar cin Kofin Duniya ta 2006 da aka yi a Berlin ta Jamus.

Gunkin 'yanwasan biyu da wani dan Aljeriya Adel Abdesseme ya yi da tagulla na da tsawon mita biyar, an girke shi a wajen cibiyar Pompidou da ke birnin na Paris.

Karon da Zidane din ya yiwa Materrzzin ya ja hankali saboda a sanadiyyarsa alkalin wasa a lokacin ya kori zidane din daga wasan wanda Italiayn ta sami nasara a bugun-daga-kai-sai-maitsaron-gida ta dauki Kofin na Duniya kuma daga wasan ne Zidane ya yi ritaya daga waga buga wasa.

An dai yi ta shaci fadi a kan abin da ya auku a tsakanin 'yanwasan biyu kafin daga bisani materazzin ya amsa da kansa cewa ya harzuka zidane din ne sakamkon wasu kalamai da ya furta a kan 'yar uwar tsohon kyaftin din na Faransa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.