BBC navigation

Gerrad ya karaya da daukar Premier

An sabunta: 30 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 19:28 GMT
steven gerrad

Steven Gerrad

Socin Kungiyar Liverpool Steven Gerrad ya fidda tsammanin za su dauki kofin gasar Premier kafin ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa, ya ce ba karamar nasara ba ce za ta sa su kai ga bajintar daukan Kofin.

Gerrad ya ce saboda shekarunsa yanzu 32 kuma ga yadda ake kara samun gwagwarmaya ga gasar daukar kofin saboda yadda sauran kungiyoyi da a da basuda karfi ba a sa su a lissafi yanzu suke tasowa.

Ya ce '' ba Manchester United ce da Arsenal kadai ba yanzu ga Manchester City da Chelsea da Tottenham, Newcastle ma na tasowa.

Kyaftin din na Ingila ya ce a bara sun kammala gasar Premier a matsayi na takwas amma a bana in har suka yi sa'a suna iya kasancewa cikin kungiyoyi 4 na farko kuma idan har hakan ta kasance a lokacin zai zama ya na da shekaru 33 kuma a badi kwantiraginsa zai kare don haka yana ganin abu ne mai wuyar gaske kungiyar ta Liverpool ta dauki Premier da shi.

Sai dai kuma duk da haka Gerrad wanda ya yi shekaru 14 a Liverpool ya ce zai yi kokari ya ci gaba da wasa kamar su Giggs da Scholes ko da shekarun nasa sun kai 33.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.