BBC navigation

Akwai 'yan mowa da bora a Premier - Aguero

An sabunta: 1 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 11:41 GMT
Sergio Aguero

Sergio Aguero na daya daga cikin manyan 'yan wasa a Man City

Dan wasan Manchester City Sergio Aguero, ya yi amannar cewa alkalan wasa na nuna son kai ga 'yan wasan Ingila kan sauran 'yan wasan da suka fito daga kasashen waje.

Aguero mai shekaru 24, ya zira kwallo daya a wasan da City ta doke Fulham da ci 2-1 - inda takwarorinsa na Argentina Pablo Zabaleta da Carlos Tevez suka nemi fanareti amma ba a basu ba.

Da aka tambaye shi ko 'yan wasan da bana Ingila ba suna fuskantar matsi fiye dana cikin gida, sai ya ce: "Wannan haka yake. Yana faruwa a ko'ina.

'Yan wasan da suka fito daga wannan kasar na samun fifiko."

Koda aka tambaye shi idan alkalan wasa na zargin 'yan wasan da suka fito daga kasashen waje, sai Aguero ya kara da cewa: "Ba mamaki. Zai iya faruwa, amma bana tunanin akwai hakan anan.

"Idan kuma akwai, to ba abin alheri ba ne ga kowa.

"A Ingila akwai 'yan kasashen waje kamar yadda ake da 'yan wasan gida, a don haka bai dace a rinka nuna banbanci a tsakani ba."

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.