BBC navigation

Keftin din kungiyar Afirka ta kudu ya yi ritaya

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:35 GMT
'Yan wasan kungiyar Afrika ta Kudu

'Yan wasan kungiyar Afrika ta Kudu

Keftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar Afirka ta kudu, Bafana-bafana, Steven Pienaar ya yi ritaya daga taka wa kungiyar leda.

Kocin kungiyar Gordon Igesund ya bayyana haka lokacin da yake sanar da sunayen 'yan wasan da za su yi wa kungiyar wasa a wasan sada zumuncin da za ta yi da kasashen Poland da Kenya a mako mai zuwa.

An yi rade-radin cewa Steven Pienaar zai yi ritaya domin ya maida hankali ga kulab din sa na Everton.

Kocin ya ce a jiya Litinin ne Keptin din ya sanar da shi ta wayar tarho game da ritayar tasa.

Steven Pienaar ya ce " ina alfaharin cewa na yi wa kasa ta wasa, kuma a matsayin keptin.

"Bayan sama da shekaru goma ina bauta wa kasa ta yanzu ina kokari ne na maida hankali ga kulab dina na Everton.

" Akwai 'yan wasa masu tasowa 'yan baiwa kuma ina ganin cewa lokaci ya yi da ya kamata a ba su dama su taka tasu rawar."

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.