BBC navigation

Ghana ta kira Paintsil don karawa da Malawi

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:24 GMT
'Yan wasan kasar Ghana

'Yan wasan kasar Ghana

An sanya John Paintsil a cikin tawagar kungiyar kwallon kafar Ghana, wacce za ta kara da Malawi a cancantar shiga gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afrika.

Za a taka ledar ne tsakanin kasashen biyu a Lilongwe a ranar 13 ga watan Octobar shekarar da muke ciki.

Inda Black Stars ta Ghana za ta yi kokarin kare matsayinta na ci biyu da nema.

Rabon da Paintsil ya bugawa kasarsa wasa tun bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afrika, wanda kasashen Gabon da Equatorial Guinea suka dauki bakuncinsa.

Kwanan nan ne dan wasan mai shekaru 31 ya koma Israila, inda yake bugawa kungiyar kwallon kafa ta Hapoel Tel Aviv wasa, bayan ya kwashe lokaci mai tsawo baya buga wasa.

Sauran 'yan wasan da Ghana ta kira zuwa gida sun hada da Jonathan Mensah da Rabi'u Muhammed dake bugawa Faransa wasa.

Sai David Addy dake bugawa Portugal kwallo da mai tsaron gida Philemon McCarthy wanda ya dawo fagen tamaula, bayan shekaru shida baya wasa.

Kodayake manajan kungiyar Kwesi Appiah ya baiwa Paintsil da Mensah tikitin komawa fagen kwallon kafa na kasa da kasa, wasu kamar dan wasan tsakiya Derek Boateng, kociyan bai dauki matakin mai dadi a kansu ba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.