BBC navigation

Najeriya ba ta cikin kasashe goma na farko —FIFA

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:28 GMT
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA, ta fitar da jerin sunayen kasashen nahiyar Afirka gwargwadon karfinsu a fagen kwallon kafa a watan Oktoba.

Sai dai Najeriya, wadda a da ta kasance a sahun karfafan kasashe a nahiyar, a wannan watan ba ta samu shiga goma na farko ba.

Najeriyar dai ita ce ta goma sha uku a jerin, yayin da kasar Ivory Coast ta zo ta farko, Algeria ta biyu, Mali kuma ta zo uku.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.