BBC navigation

Hukumar kwallon Faransa ta fusata Wenger

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 10:51 GMT
Manajan kulob din Arsenal, Arsene Wenger

Manajan kulob din Arsenal, Arsene Wenger

Manajan kulob din Arsenal, Arsene Wenger ya yi suka ga hukumar kwallon kafa ta Faransa saboda daukar Abou Diaby a wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

Hukumar ta dauki Diaby a wasan da aka kara tsakanin Finland da Belarus a watan Satumba.

Dan wasan tsakiyar ba zai buga wasanni a makonni uku masu zuwa ba, bayan raunin da ya samu a cinyarsa a gasar da aka kara ranar Asabar da ta gabata.

Diaby mai shekaru 26 ya yi ta fama da raunuka, amma ya fara kakar wasanni lafiya.

Wenger wanda tun da fari ya bada shawarar kada a dauki Diaby yace "Ina ganin an yi kuskure a sanya shi cikin tawagar kasar."

"Na cewa hukumar idan tana son Diaby ya taka leda a Spaniya to kada ya buga wasan Finland da Belarus." Inji Wenger.

Raunin da Diaby ya samu dai ya sa ba zai samu shiga wasan Champions League da za a kara da Olympiakos ba, saboda Wenger yace a bar dan wasan ya samu hutu, idan har ana so ya shiga taka ledar da za a yi da Spaniya a watan gobe.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.