BBC navigation

Roy Hodgson ya nemi afuwar Ferdinand

An sabunta: 4 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:07 GMT
Roy Hodgson

Roy Hodgson ya baiwa Ferdinand hakuri

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Ingila, Roy Hodgson ya nemi gafara daga Rio Ferdinand sakamakon wani tsegumin da ya yi a kan makomar mai tsaron bayan kungiyar lokacin da yake tattaunawa da wasu fasinjojin jirgin kasa a London.

Kocin ya tattabatar da cewa ya fada wa fasinjojin cewa babu sunan Rio Ferdinad a cikin jerin sunayen 'yan wasan da za su taka wa Ingila leda kwana guda kafin a sanar da sunayen.

Sai dai ya musanta cewa shi ya ce Ferdinad tasa ta kare a kungiyar kwallon kafa ta Ingila.

Hodgson ya ce " ban ji dadin yadda irin wannan maganar ta fito ba, kuma ina neman afuwarsa.

Jaridar Daily Mirror ce ta ba da labarin cikakkiyar tattaunawar da Mr Hodgson ya yi da fasinjojin jirgin kasan a kan hanyarsa ta zuwa kallon wasan da kulab din Arsenal ya yi da Olympiakos a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai da aka yi ranar Larabar da ta gabata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.