BBC navigation

Ingila ta sake kiran Ryan Shawcross da Aaron Lennon

An sabunta: 4 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:43 GMT
Aaron Lennon

Lennon (wanda ake gani a sama) da Ryan za su buga wa Ingila wasa

An sake gayyatar dan wasan kulab din kwallon kafa na Stoke, Ryan Shawcross da kuma takararsa na kulab din Tottenham zuwa kungiyar kwallaon kafa ta Ingila domin su buga mata wasa a karawar da za ta yi da San Marino da Poland na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a wannan watan.

Shawcross zai maye gurbin John Terry, wanda ya yi ritaya daga buga wa Ingila wasa.

Shi kuwa Aaron Lennon ana sa ran cewa zai maye gurbin dan wasan Liverpool Steven Gerrard ne, kasancewar an hana masa shiga wasa a karawar da Ingilar za ta yi da San Marino.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.