BBC navigation

Andy Murray ya cire rai da rike kambinsa

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:23 GMT
Andy Murray

Andy Murray na shakkar kare kambinsa

Shahararren dan wasan Tennis din nan, Andy Murray wanda harwayau shi ne gwani-na-gwanayen wasan Tennis a duniya ya ce da wuya ya iya ci gaba da rike kambin nasa zuwa karshen wannan shekarar.

Dan wasan dai yana mai da martani ne ga tayin da takwararsa a wasan Tennis Roger Federer ya yi ne cewar tauraruwar Andy Murray na haskawa, kuma na nuna alamun cewa zai ci gaba da rike matsayin na farko a tsakanin 'yan wasan Tennis a duniya.

Federer ya ce "Andy Murray na da jerin nasarorin da ke nuna cewa yana daidai da ya rike matsayin dan wasan Tennis na farko a duniya nan da karshen wannan shekarar ko kuma farkon shekara mai zuwa. Wasannin da zai yi nan da watanni tara masu zuwa za su ba da sha'awa kwarai da gaske, saboda yana buga tennis yadda ya kamata."

Sai dai Andy Murray ya bayyana cewa dan wasan Tennis Novak Djokovic ne ya fi cancantar rike matsayin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.