BBC navigation

Ba za a haramtawa Ashley Cole Buga kwallo ba - FA

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:24 GMT
Ashley Cole

Ashley Cole

Shugaban hukumar kwallon kafa na Ingila, David Bernstein ya ce ba za a haramtawa Ashley Cole taka leda ba, saboda ya bada hakuri.

Dan wasan bayan, mai shekaru 31 na fuskantar tuhuma bisa zargin rashin da'a a ranar Litinin.

Hakan ya biyo bayan yin amfani da kalamai marasa dadi, a kan hukumar game da hukuncin da ta yanke a shari'ar wariyar launin fata da ta shafi John Terry.

"Ya fito fili ya bada hakuri washegarin al'amarin. Ya zo ya ganni a daren jiya, kuma ya bani hakuri" Inji Bernstein.

Shugaban hukumar ya kuma kara da cewa "Cole ya yi nadama kwarai, sai da na kalle shi sosai na tabbatar da hakan, sannan na amince da afuwar tasa. Zai iya cigaba da buga wa Ingila kwallo."

Amma shawarar sanya Cole cikin tawagar Ingila da za ta buga da San Marino da kuma Poland, a wasannin cancantar shiga gasar cin kofin duniya dake tafe, ya rage ga manajan kulob din, Roy Hodgson.

Dan wasan ya buga wa Ingila wasanni 98 kuma zai cike na dari, idan ya buga wasannin guda biyu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.