BBC navigation

Bolton ta kori Coyle a matsayin kocinta

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:58 GMT
owen coyle

Owen Coyle

Kungiyar kwallon kafa ta Bolton wanderers wadda ta fado daga gasar Premier a kakar wasannin da ta gabata da kuma take mataki na 18 yanzu a gasar Championship bayan da ta ci wasanni uku kawai daga cikin goma ta kori kocinta Owen Coyle.

Coyle wanda klub din nasa ya sha kashi 2-1 a hannun Millwall ranar Asabar ya bayyana godiyarsa ga magoya baya da shugaba da mai kungiyar Eddie Davies da kuma 'yan wasan kan yadda su ka mara masa baya tun lokacin da ya dawo kungiyar.

Kocin mai shekaru 46 ya kama aiki ne a matsayin mai horadda 'yan wasan na Bolton watanni shida bayan da ya jagoranci kungiyar Burnley ta sami cigaba zuwa gasar Premier aka kuma kara masa wa'adin kwantiraginsa a sanadiyyar hakan.

A kakar wasanni ta 2010-11 Bolton ta kai matakin wasan kusa-da-na-karshe na cin kofin kalubale na FA kuma ta kammala gasar Premier a matsayi na 14 a wannnan kaka sai dai a bara suka fado daga matakin Premier abin da ya kawo karshen zamansu a wannan gasa na tsawon shekaru 11.

Daga wadanda ake ganin za su maye gurbin Coyle a matsayin kocin na Bolton sun hada da tsohon kocin Wolves Mick McCarthy da Roy Keane wanda ya jagoranci Sunderland zuwa matakin gasar Premier.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.