BBC navigation

Hukumar kurket ta dakatar da alkalan wasa shida

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 10:37 GMT
Games

Kwallon kurket

Hukumar kurket ta duniya ta yi shellar dakatarda alkalan wasa shida da ake zarginsu da rashawa.

Hukumar ta I-C-C ta ce alkalan ba za su aiki a wasanni cikin gida ko ta kasa da kasa ba , sai bayan an kamala bincike.

Wata kafar talibijin a India ta zargi alkalan wasan kurket da suka fito daga kasashen Sri lanka, Pakistan da Bangladesh da coge a gasar kurket ta twenty-twenty abunda kuma suka musanta.

Ba ko daya daga cikin wadanda ake zargi da ya kasance a cikin gasar da aka yi a makon daya gabata inda West Indies tayi nasara.

Wani kakakin hukumar ta ICC ya ce alkalan da ake zargi ba ma'aikanta hukumar bane, akwai wani kwamitin da shi keda alhakin daukar alkalan wasa kuma shine zai gudanar da binciken cikin gaggawa.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.