BBC navigation

Hukumar kwallon Ingila za ta kafa dokokin da'a

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:51 GMT
Shugaban hukumar kwallon kafar Ingila, David Bernstein

Shugaban hukumar kwallon kafar Ingila, David Bernstein

Shugaban Hukumar kwallon kafa na Ingila, David Bernstein zai fitar da dokokin ladabi da biyayya ga 'yan wasan kasar.

Hakan ya biyo bayan wasu al'amura da suka faru wadanda suka shafi 'yan wasan kasa da kasa, musamman batun dan wasan baya, Ashley Cole.

Duk dan wasan da ya karya sabuwar dokar, za a dakatar da shi daga bugawa Ingila wasa.

Bernstein ya ce "Taurarin 'yan wasa ne da ake koyi da su, saboda haka dabi'arsu na da muhimmanci sosai. Tun shekarun baya yakamata ace an fitar da wannan dokar."

Shugabannin hukumar sun gabatar da wasu halaye goma da suke son 'yan wasan su dinga nuna wa.

"Na gano wasu abubuwa biyar a lokacin da na karbi matsayin shugabancin wannan hukumar. Daya daga cikinsu shi ne girmama wa, ba wai kawai girmama alkalan wasa ba, har ma girmama juna tsakanin 'yan wasa."

Inda ya kara da cewa "Kuma ina ganin hakan abu ne mafi muhimmanci da ya kamata in maida hankali a kai, a matsayina na shugaban hukumar kwallon kafar Ingila."

Ba dai a haramtawa 'yan wasa bayyana ra'ayoyinsu a dandalin sada zumunta na Twitter ba, amma hukumar za ta ladaftar da duk wanda ya keta sabuwar dokar da ake gaf da fitar wa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.