BBC navigation

An yi waje da Mcllroy zakaran golf na duniya

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:22 GMT
rory mcllroy

Rory Mcllroy

Zakaran wasan golf na duniya Rory Mcllroy ya fice daga gasar wasan ta duniya da a ke yi a kasar Turkiyya bayan da ya yi rashin nasara a wasansa na uku a jere.

Bayan da ya yi rashin nasara a karawarsa da Matt Kuchar da Charl Schwartzel zakaran na bukatar ya ci wasansa da tsohon zakaran wasan na duniya Tiger Woods a karawarsa ta karshe amma sai hakan ba ta samu ba Woods din ya yi galaba a kansa.

Duk da wannan rashin nasara da ya samu Mcllroy zai karbi kudi dala 300 000 ta matsayin da ya kawo.

Yanzu kuma sai wasannin kusa da na karshe tsakanin Tiger Woods da Justin Rose ya yin da Lee Westwood zai raba gari da tsakuwa tsakaninsa da Charl Schwartzel

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.