BBC navigation

Bale ya fi dacewa da Real Madrid in ji Suker

An sabunta: 15 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:49 GMT
gareth bale

Gareth Bale

Tsohon dan wasan Real Madrid kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta Crotia Davor Suker ya ce yana ganin dan wasan Tottenham Gareth Bale ya fi dacewa da Real Madrid.

Suker ya ce in dai har dan wasan na Tottenham dan kasar wales ya sami damar komawa Real Madrid to kada ya tsaya wani tunani ya amsa gayyatar kawai saboda kungiya ce da ta fi dacewa da shi.

Davor Suker ya ce kungiyoyi da dama a duniya suna da tarihin gaske,Arsenal da Manchester United da Chelsea dukkanninsu manyan kungiyoyi ne amma a wurinsa Real Madrid daya ce daga cikin kungiyoyin da suka dara sa'a a duniya.

Real Madrid na daya daga cikin kungiyoyin da ake ganin sun nuna sha'awar neman Gareth bale dan shekara 23.

Kuma daman Tottenham da Real din sun kulla wata yarjejeniya tsakaninsu da ta shafi 'yan wasa da masu horad da 'yan wasa da kuma kasuwanci, amma Tottenham din ta ki bin yarjejeniyar sau da kafa inda taki amincewa bukatar Real Madrid din a kan 'yan wasanta irin su Bale.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.