BBC navigation

CAF ta haramtawa Senegal shiga wasa

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:51 GMT
wasan, senegal, da, Ivorycoast

wasan, Senegal da Ivorycoast

Hukumar Kwallon kafa ta Afrika CAF, ta haramtawa Senegal shiga wasan cin Kofin Kasashen Afrika na 2013 bayan hatsaniyar da magoya bayan kungiyar kasar suka tayar da ya sa aka dakatar da wasan kasar da Ivory Coast.

Sai dai kawo yanzu ba a san ko Hukumar ta CAF za ta sanar da karin hukuncin da ta yanke a kan Senegal din ba.

An dakatar da wasan da ake yi a Dakar din bayan mintina 74 lokacin Ivory Coast ta jefa kwallaye biyu ba ko daya a ragar Senegal, jumulla Ivory Coast na da kwallaye 6 Senegal na da 2 idan an hada da sakamakon wasan farko a lokacin.

A hukuncin da Hukumar Kwallon Kafar ta Afrika ta yanke ta tabbatarwa Ivory Coast sakamakon wasan na lokacin da aka tsai da shi wato 2-0 ta kuma bata damar wucewa zuwa gasar cin Kofin Afrikan kai tsaye a shekara maizuwa.

Daman dai kocin Senegal din Ferdinand Coly wanda ya baiwa Ivory Coast hakuri akan lamarin ya ce Senegal za ta amince da duk hukuncin da Hukumar ta CAF ta yanke.

Hukumar CAF din ta ce ta yanke hukuncin ne bisa tanadin sashe na 16 sakin layi na 20 na dokokin gasar, wanda ya tanadi cewa idan wani yanayi ya taso da ya tilastawa alkalin wasa dakatar da wasa kafin lokacin tashi saboda kutsenmagoya bayan mai masaukin baki ko kuma tada hankalin bakin 'yan wasan , kungiyar da ke gida ita ta yi asarar wasan.

Tuni daman a ranar Litinin an sanya Ivory Coast a jerin kasashen da suka tsallake da za a rarraba su rukuni-rukuni na gasar da za ayi tsaknin 19 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.