BBC navigation

'Yan wasan Ingila za su maidawa 'yan kallo kudinsu

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:27 GMT
yan wasan ingila

'Yan wasan Ingila

'yan wasan Ingila za su bada karonsu wajen biyan fam 50,000 na 'yan kallon da suka shiga kallon wasan Ingila da Poland jiya wanda ba a yi ba saboda ruwa da iska, aka dage shi zuwa yau.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila, FA, ta ce takwararta ta Poland za ta fito da wata hanya da za a bi wajen maida wa 'yan kallon da basu sami damar dawo wa kallon wasan ba yau a Warsaw kudinsu.

Hukumar ta FA a wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na Intanet ta ce za a bukaci kowana dan kallo ya aikawa Hukumar tikitinsa a Wembley, daga nan sai ta tattara su ta aikawa Hukumar Kwallon kafa ta Poland.

Ita kuma ta Poland din zata tantance tikitin da ba a yi amfani da shi ba a kuma maidawa mai shi kudinsa.

Magoya bayan Ingila 25,000 ne su ka je kallon wasan jiya a warsaw ya yin da wasu suka dawo gida saboda rashin yin wasan da ruwa ya hana ya zuwa yanzu ba a san nawa ne daga cikinsu su ka koma kallon wasan ba a yau.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.