BBC navigation

Danny Rose ya yi kira da a kakabawa Serbia takunkumi

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:19 GMT
Football

Danny Rose dan wasan Ingila

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta 'yan kasa da shekara 21 a Ingila Danny Rose, ya yi kira da a dakatar da Serbia daga buga wasanni, bayan ya yi zargin cewa 'yan kallon Serbia sun wulakanta shi a Krusevac.

'Yan kallo sun kutsa cikin fili a daidai lokacin da Ingila ta ke murnar nasarar da ta samu na ci 1-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin tarayyar turai na shekarar 2012.

Rose dan shekara 22 ya ce ana ta yi masa ihun birai tun daga farko har karshen wasan, hakan kuma ya fara ne tun a lokacin da 'yan wasa ke yin atisaye.

Ya shaidawa Sky Sports cewa ''An jefe ni sau biyu da duwatsu a kaina a lokacin da na je zan yi jifa da kwallo''

An bawa Rose jan kati bayan an tashi daga wasan, saboda kwallo da ya doka cikin 'yan kallo, sai dai ya ce 'ihun wariyar launin fatar da ake yi a zagaye na farko na wasan, bai kai munin wanda aka yi ba a zagaye na biyu''.

Rose ya ce ''Bayan minti 60, kwakwalwata gaba daya ba ta kan wasan, raina ya yi matukar baci, kuma abu ne mawuyaci ka maida hankali."

''Daga nan sai muka samu damar jefa kwallo cikin raga, bayan minti 90 da muke fuskantar wulakanci. Daga lokacin ne na kasa boye damuwa ta'' In ji Rose.

Rose ya kara da cewa ''Abinda kawai na sani shi ne, duk 'yan wasan Serbia sun zagaye ni tare da hankade ni, zan iya tunawa an mare ni sau biyu, a wannan lokacin ne na buga kwallon nan take mai busa usur ya ba ni jan kati''.

''An gama wasa amma ba a daina yin uhun birai ba'' in ji Rose

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.