BBC navigation

Afrika ta Kudu ta shirya amma da sauran aiki, in ji lgesund

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:55 GMT
yan wasan afrika ta kudu

'Yan wasan Afrika ta Kudu

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Afrika ta Kudu Gordon Igesund ya ce 'yan wasansa sun kammala kashi 70 cikin 100 na shirin tunkarar gasar cin Kofin Afrika da za a yi a kasar amma kuma duk da haka ya ce akwai sauran aiki a gabansu.

Gordon Igesund, mai horar da 'yan wasannan, dan asalin kasar Afrika ta kudu yace akwai ragowar aikin da za a yi gabannin fara gasar a watan Janairu.

Kungiyar ta kafa ta Bafana-Bafana na ci gaba da wasa takubbanta bayan ta nuna wa kasar Kenya gazawarta da ci 2 da 1 a wasan sada zumunta ranar talata.

A watan Janairu, kasar Afrika ta kudu za ta fito a karo na farko a wata gasar neman cin kwallon kafa tun shekara ta 2008, bayan ta kasa shiga gasar a shekara ta 2010 da kuma ta 2012.

Lgesund ya yi canji wurin so 3 a cikin kungiyar 'yan wasan bayan ta sha kashi da ci 1da nema da kungiyar 'yan wasan Pologne a birnin Varsovie.

Kocin ya ce akwai wasu 'yan wasa 5 ko 6 da zai maida hankali a kansu domin ya hada karfin kungiyar wuri guda".

Gasar neman cin Kofin na Afrika za ta gudanane tsakanin ranar 19 ga watan Janairu izuwa 10 ga watan Fabrairu.

Mohaman Babalala
Journaliste
Correspondent de la BBC Hausa
au Cameroun

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.