BBC navigation

Murray ya janye daga gasar Swiss

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:22 GMT
andy murray

Andy Murray

Zakaran wasan tennis na US Open Andy Murray ya janye daga gasar Swiss wadda za a fara ranar Litinin saboda rauni.

Dan wasan mai shekara 25 dan yankin Scotland wanda Novak Djokovic ya yi nasara a kansa a wasan karshe na gasar kwararru ta Shanghai Masters a karshen makon da ya wuce ya na hutawa ne kafin jerin wasannin karshen kakar wasanni.

Murray zai fafata a gasar Kwararru ta Paris da za a fara daga ranar 29 ga watan Oktoba da kuma gasar Fitattu da za a yi a London wadda ita kuma za a fara daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

A ranar Litinin ne zakaran wasan Tennis din na daya a duniya Roger Federer wanda kuma ke rike da kofin gasar ta Swiss zai fara fafatawar kare kofin inda zai fara karawa da Jeremy Chardy da kasar Faransa.

Shi dai Federer sau biyar ya na zama zakaran gasar ta Swiss a karo shida da aka yi.

Shi kuma Andy Murray wanda a bara ma ya janye daga gasar ta Swiss tun a shekarata ta 2005 da ya fara shiga bai kara shiga ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.