BBC navigation

'Yan wasa bakar fata sun bijirewa al'ada a Ingila

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:27 GMT
rio ferdinand

Rio Ferdinand

Wasu jerin 'yan wasa da dama bakaken fata sun nuna goyon bayansu ga matakin da dan wasan nan na Reading Jason Roberts ya ce zai dauka kafin wasannin gasar Premier da a kayi a karshen makon nan na kin sanya rigar wasan da ke dauke da sunan kungiyar nan mai yaki da nuna wariyar launin fata a lokacin wasannin kungiyoyinsu.

Dan wasan baya na QPR Anton Ferdinand da wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar sun ki sanya rigar mai dauke da taken kungiyar ta 'Kick it Out' kafin wasan QPR din da Everton.

Daga cikin takwarorin Anton Ferdinand din na QPR da suka ki sanya jesin sun hada da Shaun Wright Phillips da Junior Hoilett.

Kafin wannan matakin na 'yan wasan na Rangers,shima Rio Ferdinand na Manchester United dan uwan Anton din ya ki sanya rigar mai dauke da taken yaki da wariyar launin fatar lokacin wasan United din da Stoke City ranar Asabar.

Shima dan wasan Everton dan Najeriya Victor Anichebe da abokin wasansa a kungiyar Everton Sylvain Distin sun ki sanya rigar mai taken a gabanta.

A kan matakin da 'yan wasan suka dauka kungiyar Kwararrun 'yan wasa ta Ingila wadda na daya daga cikin kungiyoyin dake baiwa kungiyar yaki da nuna wariyar launin fatar a wasanni, ta ce 'yan wasan su nada 'yancin daukan matakin da suka ga ya dace a game da sanya rigar ko kin sanya ta kuma kungiyar ta kare Rio Ferdinand ganin cewa kocin Kunigyarsa Alex Ferguson na neman daukan matakin ladabtar da shi a kan kin sanya rigar.
Daukar matakin da 'yan wasan su ka yi na kin sanya jesin ya biyo bayan kalaman Jason Roberts na Readin wanda ya ce zai dauka a wasansu na karshen mako saboda ya ce a ganinsa babu dalilin da zai sanya rigar don yayata kungiyar ta yaki da nuna wariyar launin fata saboda yana ganin bata yi wani abin a-zo-a-gani ba a wannan yaki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.