BBC navigation

Kawar da wariya a kwallo zai yi wuya —Hughes

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 10:06 GMT
Mark Hughes

Kocin QPR Mark Hughes ya ce zai yi wuya a iya kawar da wariya a filin wasan kwallon kafa

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Queens Park Rangers (QPR), Mark Hughes, ya yi gargadin cewa da kamar wuya a iya kawar da wariyar launin fata daga fagen kwallon kafa dungurungum.

A karshen mako, fiye da 'yan wasa talatin daga kungiyoyi takwas masu buga wasa a Gasar Premier ta Ingila ne dai suka ki goya baya ga yekuwar yaki da wariyar launin fata a filin wasa, wato Kick It Out, ta hanyar kin sanya tufafin T-shirt na yekuwar.

Daga cikin wadannan 'yan wasa har da mai tsaron baya na kungiyar ta QPR Anton Ferdinand, wanda kyaftin din Chelsea John Terry ya furtawa kalaman nuna wariya a kakar wasanni ta bara.

A cewar Hughes, "Abu ne mai wuyar kawarwa dungurungum. Sai dai mu yi fatan a samu cimma hakan, amma fa za a sha wuya".

Abokan wasan Ferdinand, Djibril Cisse, da Shaun Wright-Phillips, da Nedum Onuoha, da Junior Hoilett, sun bi sahunsa—kafin fara wasansu da suka yi kunnen-doki biyu da biyu da Everton ranar Lahadi—wajen nuna rashin jin dadi da gazawa wajen kawar da wariyar launin fata.

'Yan wasan Everton ma sun bi sahu

Uku daga cikin 'yan wasan Everton ma—Victor Anichebe, da Sylvain Distin, da Steven Pienaar—sun ki sanya tufafin.

Hughes ya ce "Ni da a tunanina a farkon makon, kowa zai sanya tufafin.

"To amma mutane da dama sun dauki matsaya, kuma wadansu daga cikin 'yan wasan sun ji cewa suna bukatar hada hannu, wanda abu ne da nake ganin ya kamata a mutunta.

"Duk wata yekuwa da ke da manufar magance wata illa a harkar wasan kwallon kafa da ma a tsakanin al'umma tana bukatar a goya mata baya ko da kuwa masu yekuwar ba sa taka rawar da ake zaton ya kamata su taka".

Kocin Everton, David Moyes, ya marawa 'yan wasansa uku baya, ko da yake ya ce ba lallai ba ne ya amince da matsayarsu.

"Na yi magana da 'yan wasan, kuma sun ce ita ce shawarar da suka yanke", inji Moyes.

"Don haka na saurari dalilansu, na kuma shaida musu dalilan da suka sa nake ganin ya kamata su goyi bayan yekuwar, amma sun ga cewa shawararsu ita ta fi".

Rio ya fusata Ferguson

Shi kuwa dan uwan Anton, Rio Ferdinand na Manchester United, ya gamu da fushin kocinsa ne Sir Alex Ferguson, saboda ya zabi ya ki sanya tufafin kafin wasansu da Stoke ranar Asabar.

Ferguson ya ce ya ji tamkar Rio ya kunyata shi da shawarar tasa sannan kuma ya ba da kungiyar alhalin ranar Juma'a ya ce "ya kamata kowa ya hada kai".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.