BBC navigation

An kwace kambun Lance Armstrong na Tour de France

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:32 GMT
Lance Amstrong

Lance Amstrong

Hukumar kula da wasan tseren keke ta kasa da kasa ta amince da dukkanin sakamakon binciken da hukumar yaki da amfani da miyagun kwayoyi ta Amurka ta yi a kan Armstrong.

Shugaban hukumar, Pat McQuaid, ya ce "Lance Armstrong ba shi da wajen zama a harkar wasan tseren keke, don haka ya kamata a manta da shi kawai".

McQuaid ya kara da cewa, an kwace wa Armstrong dukkanin lambobin yabon da ya samu tun daga ranar 1 ga watan Augustan shekarar 1998, an kuma haramta masa shiga gasar gaba daya.

A wani abu da ya kira rana mai dimbin tarihi ga tseren keke, shugaban hukumar dan asalin kasar Ireland, wanda ya dare kujerar tun a shekarar 2005, ya ce ba zai bar mukamin sa ba.

Hukumar yaki da amfani da miyagun kwayoyi a tsakanin 'yan wasa ta Amurka ta haramtawa Amstrong, dan kimanin shekaru 41 da haihuwa, shiga wasannin tseren keke har abada, saboda abin da ta kira dabarar amfani da kwayoyi mafi girma a tarihin wasanni a duniya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.