BBC navigation

An kara samun karin fasahar bakin raga

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:56 GMT

Raga

An kara matsawa kusa da samun fasahar bakin raga, bayan da hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, wato FIFA, ta amince da wasu na'urori guda biyu.

Hukumar ta FIFA ta ba da lasisin amfani da na'urori biyu na fasahar bakin raga a fadin duniya. Hakan na nufin cewa kamfanonin Hawk-eye da Goalref za su iya samar da na'urorin na su don amfanin gasa.

A cewar kakakin FIFA, "wannan muhimmin ci gaba na nufin cewa, a yanzu kamfanonin sun sami amincewa su girke na'urorin su a ko ina a duniya."

Na'urar Hawk-eye tana amfani ne da kyamarori guda shida wadanda ke fuskantar kowanne turke na raga, suna bibiyar yadda kwallo ke yawo a cikin fili.

Daga nan sai manhajar na'urar ta yi amfani da wata fasaha ta nuna hakikanin inda kwallon ta ke, idan kwallon ta tsallaka layin bakin raga, sai na'urar ta aike da wani sako ga agogon hannun alkalin wasa wanda zai nuna cewa an ci kwallo.

Gaba ki daya wannan aikin da na'urar ta ke yi ta na kammala shi ne a kasa da dakika daya, kamar yadda hukumar ta FIFA ta bukata.

Ana sa ran amfani da wannan fasaha a karo na farko a watan Disamba yayin gasar cin kofin kungiyoyin kwallon kafa na duniya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.