BBC navigation

Kwallon kafa za ta magance wariyar launin fata-Martin

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:32 GMT

Yaki da wariyar launin fata

Martin Offiah ya yi amanna cewa harkar kwallon kafa za ta iya magance matsalar wariyar launin fata idan ta zama kamar wasan sada zumunta tsakanin dangi kamar yadda wasan kwallon zari-ruga yake.

Offiah ya shaidawa BBC cewa ya gana da wani masoyin Kungiyar Hull a shafin Twitter wanda ya nemi afuwarsa saboda tsattar da yau da ya yi don nuna kyama shekaru ashirin da suka wuce.

Offiah wanda gogagge ne a harkar wasannin Kwallon zari-ruga, ya ce abin da za ka ji a filin wasannin gasar zari-ruga daban yake da na kwallon kafa.

A cewar Offiah, "a wasannin Kwallon kafa ba ma batun wariyar launin fata ba ne kawai; wasu lokuta za ka ji ana ihu ne kan mahaifan 'yan wasan ko kuma 'yan matansu".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.