BBC navigation

Serena Williams ta doke Agnieszka Radwanska

An sabunta: 27 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:41 GMT
serena williams

serena ta shiga zagayen karshe a WTA

'yar wasan tennis Serena Williams ta samu shiga zagayen karshe a gasar WTA da ake yi a kasar Spain bayan ta doke Agnieszka Radwanska.

Serena ta samu nasara ne bayan ta kada Agnieszka sau biyu a jere da ci 6-2 da 6-1 cikin minti sittin da daya.

A karawar dai Agnieszka ta nuna cewa ta galabaita, saboda ta kakare har sau uku, lamarin da ya bai wa Serena damar yi mata kaye cikin sauki.

Serena Williams ta ci kofi daban-daban har guda shida a kasar WTA a wannan shekarar, ciki har da gasar wasannin motsa jiki na duniya, wato Olympics da Wimbledon da kuma US open.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.