BBC navigation

Di Matteo ya nuna damuwa kan wasu 'yan wasa

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:39 GMT

Roberto Di Matteo

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roberto Di Matteo, ya nuna tsoron sa kan yiwuwar za su rasa Ashley Cole da kuma Frank Lampard a watan Janairu.

'yan wasan biyu dai za su samu damar rattaba hannu a kwantaragi da abokan gabar Chelsea a sabuwar shekara idan dai ba su amince da sabunta kwantaragin su ba wadda za ta kare a wannan kakar wasannin.

Di Matteo ya ce, " yana matukar damuwa amma dai haka harkar kwallon kafa ta duniya take".

Kociyan dai da yake amsa tambayoyi kan wasan su da Manchester United ranar Lahadi ya tabbatar cewa suna magana da Mikel Obi kan sabuwar kwantaragi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.