BBC navigation

Korafin Chelsea: FA ta kaddamar da bincike

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:59 GMT
Mark Clattenburg da John Mikel Obi

Chelsea ta zargi Mark Clattenburg da furta wasu kalamai ga John Mikel Obi

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Ingila, wato FA, ta fara bincike a kan zargin alkalin wasa Mark Clattenburg da Chelsea ta yi bayan ta sha kashi a hannun Manchester United da ci biyu da uku a Stamford Bridge.

Kungiyar ta Chelsea ta gabatar da koke ne a hukumance tana zargin Clattenburg da furta "kalaman da ba su dace ba" ga 'yan wasanta biyu ranar Lahadi.

Wani bangare na zargin shi ne cewa Clattenburg ya yi amfani da kalaman da ke nuna wariyar launin fata.

'Yan sanda sun ce suna duba wani korafi da aka gabatar a gabansu.

Ba a saka Clattenburg ya alkalanci wani wasa ba a karshen wannan makon.

Wata sanarwa daga kungiyar alkalan wasa ta PGMO ta ce: "PGMO ta yi amanna cewa a ko wanne wasan kwallon kafa kamata ya yi a mayar da hankali a kan 'yan wasa da wasan shi kansa a maimakon alkalan wasa.

"Mark Clattenburg na cikin fitattun alkalan wasan kwallon kafa a duniya, kuma a irin wannan yanayi, binciken kwakwa ka iya rage armashin wasa ya kuma zama rashin adalci ga kungiyoyi da magoya bayan ko wanne bangare".

Hukumar ta FA ta fitar da wata sanarwa ranar Litinin tana tabbatar da cewa ta kaddamar da bincike; sai dai ta kara da cewa ba za ta "ce komai ba baya ga haka a yanzu".

An yi amanna cewa korafin ya danganci dan wasan tsakiya na Chelsea, John Mikel Obi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.