BBC navigation

'Yan sanda sun fara bincike a kan Clattenburg

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:32 GMT
mark clattenburg

Mark Clattenburg

Hukumar 'Yan sandan birnin London ta fara gudanar da bincike akan zargin da ake yiwa alkalin wasa Mark Clattenburg na furta wasu kalamai da suka shafi nuna wariyar launin fata ga 'yan wasan Chelsea, lokacin wasan da manchester United ta yi nasara akan Celsea 3-2.

Ita ma Hukumar wasan kwallon kafa ta Ingila FA, ta fara nata binciken akan lamarin sakamakon korafin da Chelsea ta gabatar mata..

Kungiyar da Chelsea tana zargin alkalin wasan ne da furta kalaman da ba su dace ba da suka hada da na wariyar launin fata akan 'yan wasan kungiyar biyu.

Zargin da 'yan sandan su ke bincike a kansa ba kungiyar Chelsea ko Hukumar kwallon Kafa ta Ingilan ba ce ta gabatar da shi.

Tun da farko wani lauya da ake dangantawa da kungiyar 'yan wasa bakar fata Peter Herbert ya bayyana cewa ya gabatarwa Hukumar 'yan sandana korafin a rubuce.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.