BBC navigation

Sam Querrey ya lallasa Djokovic a Paris Masters

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:12 GMT
Novak Djokovic

Novak Djokovic ya sha kashi a hannun Sam Querrey

Novak Djokovic ya sha kashi a zubi uku a hannun dan Amurka Sam Querrey a zagaye na biyu na gasar Paris Masters.

Lokacin da ya lashe zubi na farko ba tare da ya sarayar da ko da kwallo daya ba, dan wasan tennis din na Serbia, wanda ke da garantin kammala shekarar nan a matsayi na farko, ya nuna alamun shi ke jan zaren wasan.

Amma Querrey, wanda shi ne na ashirin da uku a duniya, ya zage dantse ya yi zarra a zubi na biyu.

David Frrer, da Juan Monaco, da Janko Tipsarevic ma sun yi nasara a gasar ta Paris Masters.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.