BBC navigation

China za ta ginawa Malawi sabon filin wasa

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:22 GMT
Stade de l'Amitié

Filin wasa na Stade de l'Amitié a Gabon, inda aka buga wasan karshe tsakanin Zambia da ivory Coast

Nan ba da jimawa ba tawagar kwallon kafa ta Malawi za ta yi sabon gida a babban birnin kasar, Lilongwe.

Hakan ya biyo bayan shawarar da gwamnatin kasar ta yanke ne ta shiga a dama da ita a abin da ake kira diflomasiyyar filin wasa ta China.

Kasar ta China dai ta rattaba hannu a kan wata yarjejeniya ce ta gina wa Malawi sabon filin wasa na kasa na gani na fada a kan kudin da aka kiyasta sun kai dalar Amurka miliyan saba'in.

A bisa tanade-tanaden yarjejeniyar - wadda Ministan Kudin Malawi Ken Lipenga da Jakadan China Pan Hejun suka rattabawa hannu ranar Talata - China za ta samar da lamuni mai rangwamen ruwa wanda za a biya a shekaru ashirin.

Ana sa ran za a yi shekaru biyu ana gina filin wasan wanda zai dauki 'yan kallo dubu arba'in.

A cewar Ministan Wasanni na Malawi, Enock Chihana, "malawi na bukatar karin filayen wasanni; wannan filin wasa da China za ta gina kuma daya ne daga cikinsu".

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka, wato CAF, da Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA, sun soki filayen wasa biyun da Malawi ke da su yanzu haka da cewa ba su cancanci a buga wasanni a cikinsu ba.

Gine-ginen filayen wasanni da kudaden China wani muhimmin bangare ne na abin da Beijing ke kira diflomasiyyar filin wasa.

Dukka kasashe uku na baya-bayan nan da suka karbi bakuncin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Afirka - Angola, da Equatorial Guinea, da Gabon - China ce ta gina musu filayen wasa.

China ce ta samar da ilahirin kudin da aka gina filin wasa na Stade de l'Amitié, inda aka buga wasan karshe a Gasar tsakanin Zambia da Ivory Coast.

Hatta sabon filin wasa mai sheki da daukar ido wanda aka kaddamar bana a Zambia China ta samar da kudi sannan ta gina shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.