BBC navigation

Kungiyar Esperance ta gamu da cikas

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:50 GMT
youssef msakni

Youssef Msakni

Kungiyar kwallon kafa ta Esperance ta Tunisia ta gamu da cikas a shirinta na karawar zagayen farko ta cin kofin zakarun Afrika da za ta yi da Al Ahly ta Masar ranar Asabar, sabo da tiyatar da aka yiwa gwanin dan wasanta Youssef Msakni a matsarmamarsa.

Ranar Alhamis din nan ne aka yiwa dan wasan mai shekara 21 fida bayan da ya kamu da ciwon matsarmama.

Rashin dan wasan ba karamin koma-baya ba ne ga kungiyar ta kasar Tunisia wadda ke kokarin kare kofin da ta dauka bara.

Kwallaye hudu dan wasan ya ciwa kungiyar a gasar a bana.

Daman dai tuni kungiyar ta fidda rai da ci gaba da zaman gwanin dan wasan a cikinta bayan wasan cin kofin zakarun Afrikan na karshe saboda ya amince ya koma kungiyar Lekhwiya ta Qatar a watan Janairu na shekara mai zuwa.

Kuma fatan Esperance din shi ne dan wasan ya taka musu rawar karshe wajen kare kofin kafin ya tafi.

Shi dai Youssef Msakni na daya daga cikin 'yan wasan da aka zaba domin fidda gwarzon dan wasan Afrika na shekara daga cikinsu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.