BBC navigation

Ana binciken wariyar launin fata a kan dan kallo

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:45 GMT
'yan kallo

'Yan kallo

'yan sanda a London,sun fara gudanar da biciken zargin nuna alamar wariyar launin fata a kan wani dan kallo a lokacin wasan cin Kofin kalubale na Capital one, tsakanin Manchester United da Chelsea ranar Laraba.

Hotunan da a ka dauka sun nuna dan kallon yana yin wata alama da ake dangantawa da biri a lokacin wasan wanda aka yi filin wasa na Chelsea, Stamford Bridge.

Ana danganta cin mutuncin ne da dan wasan Manchester United,Danny welbeck, sai dai kawo yanzu ba a tabbatar cewa ko lalle mutumin welbeck din ya ke nufi da abin ba.

Tuni dai kungiyar Chelsea ta fara gudanar da bincike a kan lamarin inda ta ce zata nazarci hoton bidiyon.

A wata sanarwa da 'yan sanda su ka bayyana a London sun ce sun karbi kofarin zargin nuna wariyar launin fata a filin wasan Stanford Bridge kuma suna gudanar da bincike amma ba bu wanda aka kama zuwa yanzu.

Mai magana da yawun kungiyar Chelsea ya ce, idan su ka sami cikakkiyar sheda a kan lamarin za su dauki mataki kwakkwara da ya hada da na shari'a.

Wannan batun ya taso ne yanzu kuma bayan da kungiyar Chelsea ta zargi alkalin wasa Mark Clattenburg da amfani da kalaman da ba su dace ba a kan dan wasanta Mikel Obi, a wasan da Kungiyar ta yi ranar Lahadi da Manchester United, lamarin da Chelsean ta gabatar da korafinta ga Hukumar kwallon Kafa ta Ingila a kansa.

A farkon wannan shekara klub din Chelsea ya yanke wa wani magoyin bayansa haramcin rai da rai na danganta kansa da kungiyar bayan da mutumin ya amince cewa ya muzanta Didier Drogba, ta nuna wariyar launin fata.

A yanzu dai kyaftin din Chelsea John Terry, yana cikin hukuncin da aka yanke masa na haramcin buga wasanni hudu bayan da aka same shi da laifin nuna wariyar launin fata ga dan wasan QPR, Anton Ferdinanad.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.