BBC navigation

Ferguson na da shakku a kan koken Chelsea

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:38 GMT
Sir Alex Ferguson

Sir Alex Ferguson

Chelsea dai na zargin Clattenburg da nuna wariya a lokacin da Manchester United ta samu nasara akansu da ci biyu da uku a wasansu na ranar Lahadin da ta gabata.

Sir Alex ya ce "A hakikanin gaskiya ban yarda Clattenburg zai yi kalami marar dadi ba, ban yarda ko kadan zai aikata hakan ba".

Tuni dai Chelsea ta shigar da korafinta akan hakan ga kungiyar wasan kwallon kafa ta Ingila FA.

Ferguson dai ya yi wannan bayani ne gabanin wasan da za su yi da Arsenal, inda ya ce babu wani alkalin wasa da zai kaskantar da kansa ya aikata haka.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.