BBC navigation

Alkalan wasa na tunanin kauracewa Chelsea

An sabunta: 4 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:20 GMT
clattenburg da milkel

Clattenburg da Milkel

Wasu alkalan wasan gasar Premier na tunanin kauracewa wasannin Kungiyar Chelsea sabo da zargin da aka yi wa alkalin wasa Mark Clattenburg na furta kalaman wariyar launin fata a kan dan wasan Chelsea.

Tsohon alkalin wasan Premier, Clive Wilkes, ya ce wasu daga cikin tsoffin abokanan aikinsa sun damu matuka akan zargin, kuma sun fara tattaunawa suna duba yadda za su kauracewa wasannin Chelsea.

Ya ce wannan ba shi ne karon farko da Chelsea ke zargin alkalin wasa ba, akwai maganar wasu alkalan wasan a baya kamar su Anders Frisk da Graham Poll.

Wilkes, ya ce a kan wannan yanzu wasu alkalan wasan na cewa abin ya isa haka ya kamata a yiwa tufkar hanci, suna ganin an maida su karkatacciyar kuka, ba wanda ya ke kare su ba su da wani goyon baya.

Ya ce wasunsu suna tsoron fitowa su yi magana amma suna jin tsoro za a iya korarsu daga aiki idan suka bayyanawa duniya korafinsu.

Suna tunanin shiga yajin aiki amma hakan zai zama zabi na karshe idan suka rasa mafita, amma a yanzu suna ganin ya kamata su zauna da Hukumar Kwallon kafa ta Ingila da kungiyar Kwararrun 'yan wasa da Kungiyoyin wasa da kuma 'yan wasan kansu su tattauna don shawo kan matsalar da wuri.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.