BBC navigation

Ferguson ya damu da asarar United

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:13 GMT
alex ferguson

Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya damu da yadda 'yan wasan United suke kasa jefa kwallo a raga idan sun kai hari.

Da yake nuni da yadda wasan kungiyarsa da Arsenal ya kasance ya nuna takaicinsa da yadda 'yan wasansa suka yi ta barar da damar cin kwallaye yana cewa kamata ya yi a ce sun jefa kwallaye kamar hudu ko biyar, a wasan.

Bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gidan da Rooney ya zubar a wasan ya sa United din ta yi asarar irin wannan dama har guda hudu daga cikin shida da ta samu a kakar wasan Premier ta bana.

Kocin ya yi gargadin cewa hakan zai iya jawo musu asara a karshen kakar wasannin da ake ciki kamar yadda a bara suka kasa daukar Premier sabo da bambamcin yawan kwallaye tsakaninsu da Manchester City.

Ferguson ya ce ba ya son ya ga hakan ta sake faruwa a bana.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.