BBC navigation

Andy Murray zai kara da Tomas Berdych a gida

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:55 GMT
Andy Murray

Andy Murray zai yi karawarsa ta farko tun bayan zama zakaran US Open

Andy Murray zai buga gasarsa ta farko a gida tun bayan da ya lashe gasar US Open—nan ba da jimawa ba ne zai kara da Tomas Berdych a Gasar Karshe ta ATP World Tour.

Dan wasan na tennis ne ya kawo karshen zaman jiran tsammanin da Burtaniya ta yi shekaru saba'in da shida tana yi wani namiji daga cikin 'yan wasanta na tennis ya zama zakaran Babbar Gasar Tennis, wato Grand Slam.

Wannan ce karawa ta farko a zagayen karshe na kakar Babbar Gasar ta bana, wadda za a yi a filin O2 Arena da ke London.

Shi kuwa Novak Djokovic, wanda ya koma kan matsayinsa—na daya a duniya—zai kara ne da Jo-Wilfred Tsonga.

Lallasa Djokovic da Murray ya yi ne ya ba shi damar lashe Babbar Gasarsa ta farko a watan Satumba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.