BBC navigation

Suarez shi ne Messin Liverpool, in ji Rodgers

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:12 GMT
luis suarez

luis suarez

Kocin Liverpool Brendan Rodgers, ya bayyana Luis Suarez a matsayin Lionel Messi na kungiyarsa ganin irin kwazo da gwanintar da ya nuna a wasansu da Newcastle.

Suarez ne ya ramawa Liverpool kwallon da Newcastle ta jefa mata a raga a ranar a wasan da aka yi a gidan Liverpool, kuma ya kasance barazana sosai ga 'yan wasan Newcastle.

Rodgers ya ce Suarez, ya yi wasa a ranar kamar yadda Messi ya ke yi wa Barcelona, inda yake dauke hankalin abokanan karawarsu su rika kokarin hana shi sakewa ta haka kuma sauran 'yan wasan su samu su kutsa zuwa gidan abokanan karawar.

Sai dai kuma duk da yadda Kocin Liverpool din ya ke yabawa Suarez din ya koka da yadda ba su sami nasara ba a kan Newcastle din ya na cewa kamata ya yi a ce sun yi galaba a wasan ganin irin yadda suka yi wasa.

A wasannin da Liverpool ta yi tara a Premier, ya zuwa yanzu Suarez, ya ci kwallaye bakwai.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.