BBC navigation

Man City ta yanke kauna da kofin Zakarun Turai

An sabunta: 7 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:14 GMT
kocin kulub din Manchester City Roberto Mncini

kocin kulub din Manchester City Roberto Mncini

Kocin kulub din Manchester City Roberto Mancini ya ce burin 'yan kulub din na samun nasarar cin kofin gasar zakarun turai ya kare, bayan da suka yi duro da Ajax da ci 2-2.

"Kwallo ta ci, alkalan wasan ne ba su san aikinsu ba. "

Mancini

City ta na da maki biyu a cikin wasanni hudu da ta buga, kuma dole ta ci sauran wasanni biyu da suka rage domin samun nasarar ci gaba da zama a gasar cin kofin zakarun turai.

''Abin takaicin shi ne maki daya kadai gare mu, kuma ina tsammanin shi kanan mun yi sallam da kofin zakarun turai'' in ji Mancini.

Kocin na Manchester City ya kalubalanci alkalin wasan bayan da aka tashi daga wasan, inda yace ya hana Man City kwallon da suka jefa da sunan satar gida.

Kwallon da Sergio Aguero ya ci bayan Aleksandar Kolarov ya dago masa ita daga gefe ce fatan Man City na farfadowa daga ci biyun da aka yi musu, amma sai mataimin alkalin wasa ya daga tuta ya ce Aguero yayi satar gida.

''Ba ni ne na farko ko na karshe da zai yi wa alkali magana ba, a wasan kwallo hakan na faruwa''

Duk da haushin alkalan wasan da yake ji, Mancini ya amince 'yan wasansa sun taimaka wajen rasa nasarar cin wasa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.