BBC navigation

Ingila ta gayyaci wasu 'yan wasa na daban

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:50 GMT
jack wilshere

Jack Wilshere

Ingila ta gayyaci wasu 'yan wasa da suka hada da wasu matasa domin buga mata wasan sada zumunta da za ta yi da Sweden a mako mai zuwa.

Dan wasan tsakiya na Arsenal Jack wilshere, mai shekaru 20 wanda ya dawo fagen wasa bayan jiyyar rauni da ya yi ta sama da shekara daya ya sake samun gayyata.

Dan wasan tsakiya na Everton Leon Osman, mai shekaru 31, ya sami gayyata a karon farko, su ma 'yan wasan Liverpool Raheem sterling, dan shekara 17, da Jonjo Shelvey, mai shekara 20, na daga wadan da a ka gayyata don bugawa Ingilan wasa.

Kyaftin din Liverpool, Steven Gerrad, zai zama dan wasan Ingila na shida da zai yi mata wasa sau dari daya idan ya yi wasan da Sweden.

Tawagar 'yan wasan na Ingila da zata kara da Sweden din ta kunshi wasu 'yan wasa guda goma da basa cikin wadan da aka sanar za su bugawa Ingilan wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya da Ukraine da kuma Poland.

Game da Wilshere, wanda bai sake bugawa Ingila wasa ba tun da ya yi mata wasa na biyar a watan Yuni na 2011 da Switzerland, a sati biyun da suka wuce ne ya dawo bugawa Arsenal wasan Premier, da ta yi da QPR, tun watan Mayu na 2011.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.