BBC navigation

Di Matteo ya koka game da jadawalin wasanni

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:53 GMT

Di Matteo

Manajan Chelsea Roberto Di Matteo ya yi korafi game da yadda shugabannin Premier League suka ki sauya ranar da kulob dinsa zai buga da Sunderland, yana mai cewa ranar 8 ga watan Disamba da aka sanya ba ta dace ba.

Kulob din dai, wanda shi ne ke rike da kofin Champions League, zai buga wasan kusa da na karshe ne a gasar duniya a Japan ranar 13 ga watan Disamba, kwanaki biyar bayan wasan da za su yi da Sunderland; kuma hakan ne ya sanya manajan Chelsea ya yi ikirarin cewa 'yan wasansa za su yi matukar gajiya saboda matakin da Premier League ta dauka.

Ya shaida wa manema labarai cewa: "Mun yin kokari a sauya ranar da za mu buga wasa da Sunderland ta yadda hakan zai sa mu samu damar shiryawa, amma Premier League ba ta yarda ba, kamar dai yadda ta saba.''

"Don haka 'yan wasana za su gaji sosai tun da dai za mu buga wasan ne kwanaki uku kafin gasar da za mu yi a Japan''.

Di Matteo ya yi zargin cewa akwai lauje-cikin-nadi dangane da matakin da Premier League ta dauka.

Ya ce: ''Na yi matukar mamaki game da wannan batu.Ya za a yi na samu dama bayan zan tafi Japan -kuma akwai bambancin awanni tara- sannan na dawo kwanaki uku, na fara shirin buga wasa''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.