BBC navigation

Ghana ta maye gurbin Asamoah Gyan

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:37 GMT

Asamoah Gyan

Ghana ta gayyaci 'yan wasa guda biyu don maye gurbin Asamoah Gyan da Jonathan Mensah a wasan sada zumuntar da kasar za ta yi da Cape Verde ranar Laraba.

Gyan, wanda ke buga wasa a Hadaddiyar Daular Larabawa, ya samu amincewar kasarsa ce don ya halarci bikin binne mahaifiyarsa,Cecilia Amoako, wanda za a kwashe mako daya ana yi.

Shi kuwa Mensah ba zai buga wasan ba ne saboda raunin da ya ji a cinyarsa lokacin da yake buga wasa a kulob dinsa na Faransa, watau Evian.

Yanzu dai dan wasan tsakiya, Afriyie Acquah, da na gaba, Lee Addy, za su maye gurbinsu.

'Yan wasan za su je kasar Portugal ranar Litinin inda babbar kungiyar kwallon kafar kasar, Black Stars, ke horas da abokan wasansu, bayan da suka karbi umarni daga kocin kulob din, Kwesi Appiah.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.