BBC navigation

Ina zabar kananan 'yan wasa ne saboda gaba - Hodgson

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:10 GMT

Roy Hodgson

Kocin Inliga, Roy Hodgson, ya ce yana zabar kananan 'yan kwallo ne su buga wasa a babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar don samun horo saboda gaba.

Wilfried Zaha na cikin kananan 'yan wasan da Hodgson ya kira a baya-bayan nan don buga wasa a babbar kungiyar duk da cewa sau biyar kacal ya buga wasanni a rukunin 'yan kasa da shekaru 21.

Hodgson ya shaidawa shafin intanet na FiFA cewa: ''Idan ka zabi tawagar da ke kunshe da 'yan wasa 23, kana da damar saka wadansu 'yan wasan da ba su da gogewar da za su taka rawa a yanzu. Za ka yi hakan ne kana mai la'akari da cewa shekaru biyu ne suka rage mana don cancantar shiga gasar kwallon kafar duniya da za a yi a Brazil''.

Ya kara da cewa idan aka sanya kananan 'yan wasan a cikin manya za su samu kwarewa irin ta su Wayne Rooney da Steven Gerrard da kuma Ashley Cole.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.