BBC navigation

Kocin mata na Najeriya ya yi murabus

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:13 GMT

Kadiri Ikhana


A Najeriya, kocin tawagar kwallon kafa ta mata, Kadiri Ikhana, ya ajiye mukaminsa kwanaki biyu bayan tawagar ta sha kashi a hannun takwararta ta Kamaru lokacin wasan neman gurbi na uku a gasar mata ta Afrika da aka yi a Equatorial Guinea.

'Yan wasan tawagar ta Super Falcons sun gaza kare kambunsu ne, wanda suka lashe a Afirka ta Kudu a shekarar 2010, bayan da tawagar Kamaru ta ci su daya mai ban haushi a wasan kusa da na karshe.

Yanzu dai su ne ke da matsayi na hudu a Afirka, kuma wannan shi ne matsayi mafi kaskanci a gasar ta Afrika.

Ikhana ya ce: ''Na yi murabus ne saboda na gaza daukar kofin gasar. Na bai wa kasata kunya, don haka na dauki alhakin wannan gazawa, kuma ina neman afuwa saboda abin da na jawo wa kasata a Equatorial Guinea''.

Duk da cewa Ikhana ya cika sharudan da aka gindaya masa a kwantiragin da ya sanyawa hannu, ya ce hakan bai isa ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.