BBC navigation

Mai yiwuwa Lampard ya koma China

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:26 GMT

Frank Lampard

Mataimakin shugaban hukumar gudanarwar kulob din Guizhou Renhe, Yang Xiayou, ya ce sun fara tattaunawa da dan wasan Ingila, Frank Lampard, a kan yiwuwar komawarsa kulob din.

Idan Lampard ya koma China, zai tarar da abokansa na Chelsea da suka koma can irinsu Didier Drogba da Nicolas Anelka.

A makonnin baya-bayan nan dai, an yi ta rade-radin cewa Lampard da Ashley Cole za su bar Stamford Bridge ganin cewa kwantaraginsa ta kusa karewa.

Jami'in Rehne ya shaidawa wani gidan talabijin na Beijing mai suna BTV-6 cewa: "Eh, muna tattaunawa da Lampard, sai dai har yanzu ba mu cimma matsaya ba''.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.