BBC navigation

An rage 'yan kallon da za su shiga filin wasan Tunisia

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:53 GMT

'Yan kallo a filin wasan Tunisia

Hukumomi a kasar Tunisia sun ce za su rage yawan mutanen da za su shiga filin wasan Rades da ke birnin Tunis ranar Asabar lokacin da za a buga zagaye na biyu a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Afrika

Hukumomin sun sayar da tikiti 35,000 ne ga masu son kallon wasa, duk da cewa filin wasan zai iya daukar mutane 65,000.

Ana ganin sun yi haka ne don gujewa barkewar rikici.

Kulob din kasar, Esperance, ya sha alwashin lashe gasar a karo na biyu a jere.

Kulob din da abokin hamayyarsa na Masar, watau Ahly sun tashi ne da ci daya da daya a wasan da suka buga a zagayen farko na gasar.

Zanga-zangar da aka yi a kasashen Larabawa ta samo asali ne daga Tunisia kusan shekaru biyu da suka gabata, lamarin da ya sanya hukumomi suka hana taron jama'a a filayen wasa don gudun barkewar tarzoma.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.