BBC navigation

Manchester United ta nuna sha'awa a kan Zaha

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:34 GMT

Wilfried Zaha

Kocin Manchester United na shirin bayyana sha'awarsa ta sayen dan wasan Crystal Palace, Wilfried Zaha, amma zai bar Zaha ya ci gaba da kasancewa a kulob dinsa har karshen kakar wasa ta bana.

Sir Alex Ferguson ya shafe watanni da dama yana sanya idanu kan yadda dan wasan mai shekaru 20 ke buga wasanni, kuma ya gamsu da yadda yake taka leda, musamman irin rawar da ya taka lokacin da kulob din Palace ya yi nasara a wasansu da Leicester ranar 27 ga watan Oktoba.

Arsenal, da Liverpool, da Manchester City da kuma Tottenham sun sa idanu kan yadda Zaha ke taka leda, kuma suna jiran zuwa watan Janairu, lokacin da ake sayen 'yan wasa don nuna sha'awar su ta sayen sa.

Zaha dai na cikin 'yan wasan da za su bugawa Ingila wasan sada zumuntar da za ta yi da Sweden a ranar Laraba.

Kwantaragin da Zaha ya sanyawa hannu a Palace za ta kare ne a shekarar 2017, kuma daya daga cikin jami'an kulob din, Steve Parish, ya ce duk kulob din da ke son sayen dan wasan dole ne ya biya fam miliyan 20.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.