BBC navigation

Whelan ya goyi bayan bullo da sababbin tsare-tsare

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:19 GMT
Dave Whelan

Dave Whelan

A karkashin dokar, wadda mai yiwuwa za a bullo da ita a kakar wasanni ta badi, ba za a bari kungiyoyin kwallon kafar su rika kashe kudade fiye da kima ba.

Whelan ya shaidawa BBC cewa: "Ina kyautata zaton kungiyoyin za su ce suna bukatar wannan doka".

Wannan doka dai za ta kawo gagarumin sauyi a Gasar ta Premier, inda alal misali zakarar Gasar, wato Manchester City, ta yi asarar fam miliyan dari da casa'in da bakwai, kamar yadda raskwana ta baya-bayan nan ta nuna Sakamakon irin Kudaden da ta kashe.

Kungiyoyin wasan kwallon kafar Premier dai sun tafka asarar jimillar fam miliyan dari uku da sittin da daya a kakar wasanni ta shekarar 2010 zuwa 2011.

Wakilan manyan kungiyoyi ashirin na Gasar za su tattauna ranar Alhamis da masu ruwa da tsaki a bangaren ta yadda za a sanya ka'idoji a bangaren kudi.

Dave Whelan wanda ya mallaki kulob din Wigan dake wasa a gasar Piremiyan Ingila, ya ce ya yi amannar kulob-kulob na Piremiyan za su amince da sabuwar dokar da za ta kawo sauye-sauye a gasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.